Mugabe ya dawo daga duba lafiya a ketare | Labarai | DW | 05.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mugabe ya dawo daga duba lafiya a ketare

Shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe ya koma gida Harare a wannan Lahadi bayan ziyartar likitoci da ya yi a kasar Singapore don duba lafiyarsa.

Shugaba Robert Mugabe ya kasance a kasar ta Singapore ne tun a ranar Laraba da ta gabata kwanaki kalilan da bikin cikarsa shekaru 93 a duniya, ziyarar da jami'an kasar suka ce ta ganin likita ce kamar yadda ya saba.

Bayanai sun ce a fitar da ya yi ranar 25 ga watan jiya, an ruwaito karancin kuzari a tare da Shugaban na Zimbabuwe, batun ma da ya kai ga tsare wasu 'yan jaridun kasar da suka labarta labarinsa da tsanani. Ko da yake an saki 'yan jaridun su biyu daga bisani, an zargesu ne da rage kimar Shugaba Mugabe. 

Batun rashin lafiyar Shugaba Robert Mugabe dai batu ne da ke daukar hankali a 'yan shekarun baya-bayan nan a Zimbabuwa musamman ma ganin yadda yake ziyartar kasar ta Singapore a kai a kai.