Mugabe na shan suka kan mukamin WHO
October 21, 2017Babban daraktan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana bada wannan mukami a babban taron yaki da cutattuka da ba sa bazuwa (NCDs) a Yurugai ranar Laraba. Shugaba Mugabe mai shekaru 93 a duniya da kasashen Yammacin duniya da 'yan kasarsa ke tuhuma kan lalata harkokin lafiya a kasarsa, da take hakkin bil Adama a cewar Iain Levine, mataimakin darakta a kungiyar Human Rights Watch, ba shi wannan mukami da ya cancanci mutane da suka yi fice a tallafin al'umma abin kunya ne.
Mai magana da yawun Hukumar Lafiyar ta Duniya kuwa Christian Lindmeier ya ce shugaban hukumarsu na bukatar masu fada a ji ne a harkokin kula da lafiya da hukumar ta sa a gaba. Jami'an diflomasiya dai daga Yammacin Duniya sun sha mamaki na bayyana sunan na Mugabe cikin jagororin wannan tafiya ta wayar da kan al'umma kan wadannan cutattuka da ba a baza su.