Mugabe: Har yanzu ba a sami chanji na ba. | Labarai | DW | 19.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mugabe: Har yanzu ba a sami chanji na ba.

Shugaban Zimbabuwe ya ce an gaza samun wanda zai gaje shi a kan mulki abin da ya janyo yake ci gaba da rike madafun iko.

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabuwe ya bayyana cewa jam'iyyar ZANU-PF da jama'ar Zimbabuwe sun gaza samun wanda zai gaje shi a zaben shekara ta 2018. Shugaban ya yi kalaman ne yayin da ake shirin bikin cikarsa shekaru 93 da haihuwa.

Mugabe ya shaida wa kafofin yada labaran Zimbabuwe cewa gabilin mutanen kasar sun tabbatar da cewa babu wanda zai iya maye gurbinsa, wanda ya sa suka amince da shi.

Shugaba Robert Mugabe yana rike da madafun ikon kasar ta Zimbabuwe tun shekarar 1980 lokacin da kasar ta samu 'yanci daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya, kuma jam'iyyar mai mulki ta tabbatar da Mugabe a matsayin dan takara a zabe mai zuwa na shekara ta 2018.