1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mubayi'ar kasashe ga Birtaniya kan Rasha

Abdullahi Tanko Bala
March 27, 2018

Kawo yanzu sama da kasashe 20 suka bi sahun Birtaniya wajen daukar matakin korar jami'an diflomasiyyar Rasha dangane da zargin sanyawa tsohon jami'in leken asirin Rashar dake Zaune a Birtaniya guba

https://p.dw.com/p/2v4mo
Wladimiir Putin im Interview mit der französischen Zeitung Le Figaro in Paris
Hoto: Reuters

Kasashe da dama sun sanar da aniyarsu ta korar jami'an diflomasiyyar Rasha bayan matakin da Birtaniya ta dauka na korar ma'aikatan diflomasiyyar kasar ta Rasha sakamakon zargin sanyawa wani tsohon jami'in leken asirin Rashar dake zaune a Birtaniya guba a farkon wannan watan.

A jiya litinin ma shugaban Amirka Donald Trump ya bada umarnin korar jami'an diflomasiyyar Rasha su kimanin 60 tare da rufe karamin ofishin jakadancin Rasha da ke Seattle.

Kasar Ukraine ta kori jami'an Rasha 13 a cewar shugaban kasar Petro Proshenko, yayin da Poland ta zayyana wasu jami'an Rasha hudu wadanda ta ce suna zaman kansu ne domin ba za ta amince da su a matsayin jami'an diflomasiyya ba.

Sauran kasashen Turai da suka bi sahun hadin kai da Birtaniya wajen daukar mataki kan Rasha dangane da wannan al'amari sun hada da Denmark da kuma Netherlands da kasashe shidda da ke cikin kungiyyar EU wadanda suka hada da Latvia da Estonia da Finland da Romania da Croatia da kuma Sweden.

Kasar Austaraliya ita ce kasa ta baya bayan nan da ta kori jakadun diflomasiyyar Rasha a matakin martani ga hari da sinadrin guba da aka sanyawa wani tsohon jami'in leken asirin Rasha tare da 'yarsa a Birtaniya wanda ake zargin Rasha da aikatawa.

Angela Merkel und Wladimir Putin in Berlin
Hoto: Getty Images/S. Gallup

Firaministan Australia Malcom Turnbull ya ce ma'aikatan diflomasiyyar biyu na Rasha da aka kora jami'ai ne na leken asiri da ba'a baiyana su ba, kuma an basu wa'adin kwanaki bakwai szu tattara ya nasu ya nasu su fice daga kasar Australia. Turnbull ya shaidawa manema labarai a Canberra babban birnin kasar cewa gwamnatinsa ba za ta tsaya ta zuba ido tana kallo wata kasa tana keta alfarmar kasashe aminanta ba.

" Wannan batu ne na abinda gwamnatin Rasha ta aikata kuma batu ne na muradin tsaron kasarmu wanda za mu ci gaba da karewa. Ba za mu yarda ba kuma ba zamu tsaya mu zuba ido ba a yayin da ake keta yancin cin gashin kai na kasashe aminan mu tare da yi musu barazana ba. Wannan shi yasa muka dauki matakin da muka zartar a yau."

Jami'ai a ofishin jakadancin Rasha a Canberra sun zargi hukumomin Australia da sahun Birtaniya wajen korar jami'an diflomasiyyar Rasha biyu ba tare da yin cikakken nazari da hankali ba. Jakadan Rasha a Australiar Grigory Logvinov, yace matakin zai dagula kyakyyawar huldarjakadanci dake tsakanin kasashen biyu. Clip......

" A gaskiya ban shirya baiyana ko wane irin mataki Rasha za ta mayar ba, amma tabbas akwai martani da za'a mayar ga halayyar kasashen yamma wanda abin takaici kasar Australia ta shiga ciki, wanda kuma muke gani babu adalci a cikinsa kuma bai dace da dokokin kasa da kasa ba."

Großbritannien Theresa May, Premierministerin
Hoto: Reuters/Parliament TV

Tun da farko Firaministar Birtaniya Theresa May ta shaidawa majalisar dokokin Birtaniyar cewa tsohon jami'in loeken asirin na Rasha tare da 'yarsa da aka sanya wa guba suna kwance a asibiti cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.

"Sergei da Yulia Skripal har yanzu suna nan a asibiti cikin mawuyacin yanayi, abin bakin aciki a makonm da ya wuce likitoci sun nuna cewa a yanayin da suke ciki zai wuya su iya warkewa nan kusa, ko ma watakila ba zasu iya warkewa baki daya ba."

Ya zuwa yanzu dai Birtaniya da kawayenta sun kori jami'an diflomasiyyar Rasha kimanin 130.

Sai dai a waje guda wani lauyan Amirka Bruce Fein ya ce wannan mataki ya jefa kasashen cikin wani sabon yaki na cacar baka.