Mtsalolin Kudi Da ′Yan Kaka-Gida Kan Fuskanta A Nan Jamus | Siyasa | DW | 08.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mtsalolin Kudi Da 'Yan Kaka-Gida Kan Fuskanta A Nan Jamus

Da yawa daga 'yan kaka-gida daga Rasha su kan fada cikin mawuyacin hali na kaka-nika-yi da dimbim bashin dake kansu sakamakon rashin wata cikakkiyar masaniya a game da tsarin dokokin Jamus

A sakamakon rashin wata takamaimiyar masaniya a game da tsarin dokokin Jamus da yawa daga Rashawa ko kuma tsattsan Jamusawa da kan yi kaura daga tsofuwar tarayyar Soviet zuwa nan kasar su kan samu kansu a cikin mawuyacin hali na matsalolin kudi. Yawa-yawanci su kan fada cikin wannan mawuyacin hali ne sakamakon tallace-tallace da ake yi a telebijin da sauran kafofin sadarwa. Misali wani matashin da ya kulla yarjejeniya da wata kungiya ta motsa jiki, amma ko sau daya bai leka zauren domin cin gajiyar na’urorin da aka tanadar ba. Watanni kalilan bayan haka aka rika aika wa mahaifiyarsa takarda domin ta biya bashin dake kan wannan yaro, amma ita uwar yaron bisa ga ra’ayinta ba lalle ba ne ta biya wadannan kudi saboda ko sau daya dan nata bai yi amfani da yarjejeniyar ba. Wannan kuwa babban kuskure ne wanda ala tilas ta nemi taimako daga hukumar wayar da kan jama’a a game da matsaloli na basussuka. Akalla dai hukumar ta samu kafar shiga tsakani domin cimma wata manufa mai sassauci tsakaninta da masu wannan klob. Wata malamar makaranta ‚yar usulin Rasha da ta yiwo kaura zuwa nan Jamus a 1991 Nina Diehl a takaice tana da cikakkiyar masaniya a game da ire-iren wadannan matsaloli a sakamakon haka dake ba da shawara a kwasakwasan koyan harshen Jamusanci da take shiryawa. Ta ce sama da mutane 400 ne kan nemi shawara daga wajenta a shekara. Nina Diehl ta kara da cewar wani abin da kan jefa ‚yan kaka-gidan na Rasha cikin matsaloli na kudi shi ne kayayyakin da mutum ke iya saya akan ba shi kamar dai mota ko kayan alatu na gida, da zarar mutum ya kasa biyan basussukan sakamakon asarar aikinsa sai ya shiga kaka-nika-yi. Wannan matsala ce da ta shafi kowa da kowa ba wai wani jinsi na mutane kadai ba. Sai kuma matsalar yare, saboda a nan ne take kasa tana da bo. Domin kuwa rashin iya yaren na ma’anar rashin fahimtar ainifin abin da yarjejeniyar da aka kulla wajen wanzar da cinikin ta kunsa. Ita matsalar ba a nan kawai ta tsaya ba. Sau tari su kansu Rashawa ‚yan kaka-gidamn akan kware su wajen kin biyansu hakkinsu saboda rashin fahimtar yare. Ta la’akari da haka Nina Diehl, a shawarwarin da take bayarwa ta hada da fassara da kuma wayar da kan jama’a game da al’amuran doka da abubuwan da yarjeniyoyin cinikin suka kunsa. A cikin wata shawarar da take ba wa ‚yan kaka-gidan tayi musu kashedi a game da garaje wajen kulla wata yarjejeniya ta sayen kaya akan bashi mutum mutum ba ya da aiki na dindindin. Wajibi ne a yi sara tare da duban bakin gatari, in kuwa ba haka ba mutum zai wayi gari murnarsa ta koma ciki, a maimakon wadatar arziki da walwalar rayuwa da yake fatan samu sai ya fada cikin mawuyacin hali na matsalolin kudi da dimbim bashi akansa.