1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mr Zuma na fama da zarge-zargen cin hanci da rashawa

Shugaban Jam´iyyar ANC a Afrika ta Kudu, Mr Jacob Zuma ya ce har yanzu babu wata tuntuɓa da akayi ma sa, dangane da zargin cin hanci da rashawa. A jiya mai gabatar da ƙara, Mr Mokotedi ya tabbatar da cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da zargin cin hanci da rashawa da akewa Mr Zuma. Jami´an ya tabbatar da cewa akwai ƙwararan hujjoji da za su haifar da gurfanar da Mr Zuma a gaban ƙuliya. Tuni dai magoya bayan Zuma su ka yi watsi da zarge-zargen da cewa siyasa ce kawai a ciki. A ranar talata ne Mr Zuma ya kayar da shugaba Thabo Mbeki a zaɓen shugaban Jam´iyyar ta ANC da aka gudanar. Hakan dai na a matsayin sharar fage ne ga Mr Zuma na zamowa shugaban ƙasar a shekara ta 2009.