1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mr Sharon ya gudanar da taron farko na sabuwar jam´iyyar sa

November 24, 2005
https://p.dw.com/p/BvJc

Faraministan Israela Mr Arial Sharon ya gudanar da taron sabuwar jamiyyar sa na yan mazaman jiya dake a matsayin na farko a tun lokacin daya fice daga jamiyyar Likud.

A lokacin wannan taro, yan jamiyyar sun amince da sawa sabuwar jamiyyar suna KADIMA, wanda ke nufin gaba dai gaba dai da harshen Hebrew.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa mutane a kalla 144 ne suka rattaba hannun amincewa da wannan sabon suna a matsayin iyayen sabuwar jamiyyar.

A waje daya kuma, bayanai sun shaidar da cewa jamian zartarwa na jamiyyar Likud sun tsayar da 19 ga watan disamba a matsayin rana da zasu zabi, wanda zai maye gurbin Arial sharon a matsayin shugaban jamiyyar.

An dai cimma wannan matakin ne bayan wani taro da jamian jamiyyar suka gudanar a can birnin Tel Aviv a yau alhamis.

Mutanen dai da ake kyautata zasu kara wajen neman wannan mukami, sun hadar da ministan harkokin waje na kasar wato Silvan Shalon da ministan tsaro wato Shaul Mofaz da kuma tsohon Faraministan kasar wato Benjamin Netanyahu , wanda ake ganin shine ka iya lashe wannan zabe.