1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mr sharon ya fara farfadowa

Faraministan Israela Ariel Sharon ya fara numfashi da kansa, yayin da likitocin dake duba shi suka fara dawo dashi cikin hayyacin sa, bayan sumar dashi da suka yi, don gudanar da tiyata a kwakwalwar sa.

Babban daraktan asibitin da aka kwantar da Mr sharon , wato Mor Yosef ya tabbatar da cewa , har yanzu Mr sharon na cikin mawuyacin hali,bisa hakan dawo dashi cikin hayyacin sa baki daya zai dauki yan kwanaki kadan.

Duk da wannan ci gaba da aka samu a cewar babban likitan , Mr Sharon naci gaba da samun taimakon na´urori ne, wajen yin numfashin.

Kwararrun a wannan fanni sun yi nuni da cewa abu ne mai wuya Mr Sharon ya koma bakin aikin sa, bisa irin halin da yake faruwa game da lafiyar sa a halin yanzu.

Idan dai za a iya tunawa, Mr Sharon ya samu bugun zuciya ne mai karfi, wanda ya haifar masa da tsinkewar jini a kwakwalwar sa a makon daya gabata, wanda hakan yayi sanadiyyar yi masa tiyata har sau uku a kwakwalwar tasa.