Mr Musharraf na jiran hukuncin kotun koli
October 7, 2007Manyan alkalan kotun kolin Pakistan na nazarin kundin tsarin mulkin kasar, don tantance sahihancin takarar shugaba Pervez Musharraf, a zaben shugaban kasa daya gudana a jiya.Hakan kuwa yazo ne, bayan ci gaba da tababar nasarar da Mr Musharraf din ya samu ne a zaben na shugaban kasa, a yayin da yake rike da ragamar rundunar sojin kasar.
Tuni dai Mr Musharraf ya magantu, don ganin cewa ba´ayi masa sakiyar da ba ruwa ba:
Mr Pavez Musharraf yace ko da akwai adawa ko akasin haka, dimokradiyya itace mulki na mafiya rinjayen jama´a, a don haka shine ya lashe wannan zabe, bayan samun kashi kusan 54 zuwa 55, na kuriun da yan majalisun dokokin kasar suka ka da:
Tuni dai hukumar zabe ta kasar tace, dole ne sai Mr Musharraf ya samu tubarrakin kotun kolin kasar, kafin ya tabbata cewa shine ya lashe wannan zabe na jiya asabar.