Mr Ehud Olmert ya karbi ragamar shugabanci a Israela | Labarai | DW | 11.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mr Ehud Olmert ya karbi ragamar shugabanci a Israela

Jami´an zartarwa na kasar Israela sun amince da nadin Mr Ehud Olmert a matsayin faraministan kasar.

Nadin na Mr Olmert dai ya biyo bayan irin hali ne na rashin cikakkiyar lafiya ta faraminista Mr Ariel Sharon, wanda hakan ya tabbatar da cewa ba zai iya aikin ba.

Mr Ehud Olmert, wanda yake shugabantar jamiyyar Kadima, da faraminista Sharon ya kirkiro, a yanzu haka ya mayar da hankali ne wajen kafa gwamnatin hadaka, bayan samun nasarar zabe da jamiyyar sa tayi.

A dai zaben na ranar 28 ga watan maris na wannan shekara da muke ciki, jamiyyar ta Kadima, ta kasance ja gaba a yawan kuriu, a zaben gama garin da aka gudanar, wanda hakan ya bata damar kafa gwamnatin hadaka.