Mr Castro ya fara samun sauki... | Labarai | DW | 02.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mr Castro ya fara samun sauki...

Rahotanni daga asibitin da aka kwantar da shugaban kasar Cuba, Fidel Castro na cewa, shugaban na cikin koshin lafiya, bayan nasarar da aka samu nayi masa tiyata a cikin cikin sa.

Mr Castro, wanda yake cika shekaru 80,ranar 13 ga watan nan ya mika ragamar tafiyar da harkokin mulkin kasar na wucin gadi ga dan uwan sa ne a ranar litinin din data gabata ne, wato Mr Raul.

Ya zuwa yanzu dai kafafen yada labaru, sun rawaito kakakin fadar white house, wato Mr Tony Snow na cewa Amurka ba zata canza matakan ta ba a game da kasar ta Cuba, sakamakon abubuwan da suke faruwa a kasar a halin yanzu.