Mr Anan zai kai ziyarar gani da ido izuwa kudancin Libanon | Labarai | DW | 29.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mr Anan zai kai ziyarar gani da ido izuwa kudancin Libanon

A yau ne a nan gaba kadan sakataren Mdd Mr Kofi Anan ya shirya kai ziyara izuwa kudancin Libanon , don ganewa idanun sa irin barnar data faru a lokacin yakin da aka gwabza a tsakanin Hizboullah da Israela.

Mr Anan , wanda ya fara ziyarar aiki izuwa yankin gabas ta tsakiya a jiya, yayi kira ga Israela data kawo karshen kawanya ta ruwa da sama data yiwa Libanon, don isar kayayyakin agaji ga fararen hula na kasar.

Bugu da kari sakataren na Mdd, ya kuma bukaci kungiyyar Hizboullah data saki sojin Israela biyu data cafke a watan yuli, wanda hakan na daya daga cikin dalilan daya haifar da wannan yaki.

Rahotanni dai sun nunar da cewa, akwai kyakkyawan fata da ake cewa Mr Anan zai kai ziyara izuwa kasar Israela a wannan rana ta talata, don saduwa da shugaba Ehud Olmert.