1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mozambique ta cika shekaru 30 da samun yancin kai

Hauwa Abubakar AjejeJune 24, 2005

kasar mozambique tana bikin cikarata shekaru 30 da samun yancin kai daga kasar Portugal

https://p.dw.com/p/Bvb6

A gobe asabar ne idan Allah ya kaimu,zata yi bikin cikar shekaru 30 da samun yancin kanta daga kasar Portugal da tayi mata mulkin mallaka.

Za ayi bikin ne na gobe a wajen kaburburan wadanda suka sadaukar da kansu ga samarwa kasar yancin su 26,ciki har da shugabanta na farko Samora Micheal.

Shugabannin kasashe da ake sa ran zasu halarci bikin kuwa sun hada da shugaban kasar Botsawana,da na Namibia da Tanzania da kuma Nelson Mandela wanda yanzu yake auren uwargidan marigayi Samora Micheal,wato Gracia Micheal.

Shi dai Samora Micheal ya rasu ne cikin wani hadarin jirgin sama da ya rutsa da shi a kasar ATK makwabciya a 1986,wanda ake ganin dakarun gwamnatin wariyar alumma ne suka harbo jirgin.

A wancan lokacin gwamanatin kasar mai jamaa milyan 18 da farar fata suka mamaye ta yi kokarin rage yawan talauci daga kashi 69 cikin dari a shekarun da suka biyo bayan yakin basasar kasar zuwa kashi 54 da ake da shi yanzu.

Tsohuwar kungiyar yan tawaye ta RENAMO wadda ta rikida zuwa jamiyar adawa bayan karshen yakin a 1992ta ce baza ta halarci bikin ban a gobe maimakon haka ta shirya zata yi nata bukukuwan dabam a dukkan larduna 11 na kasar,tana mai cewa fakewa ne jamiyar da ke mulkita FRELIMO take yi da wannan biki domin ta kara samun magoya baya.

Mai Magana yawun jamiyar adawa Fernando Muzanga ya ce taron shagali ne nay an jamiya kawai ita jamiyar da ke mulki ta shirya,yana mai cewa bai dace ba ace zaa nufi dandalin yanci dauke da tutar jamiyar da ke mulki wanda ya ce hakan son kai ne.

Ita dai jamiyar ta FRELIMO ita ke mulkin kasar ta Mozambique tun samun yancin kanta.Bayan mutuwar Samora Micheal,sai Joachim Chissano ya karbi ragamar mulkin kasar inda ya kai kasar ga samun zaman lafiya ya zuwa yanzu.A bara ne kuma ya sauka daga kan karagar mulkin kasar inda wani attajiri dan kasuwa Armando Guebuza ya gaje shi.