Mouhmadou Issoufou: Ba zan yi takara ba | Labarai | DW | 02.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mouhmadou Issoufou: Ba zan yi takara ba

Shugaban Jamhuriyar Nijar ya ce babu batun taba kundin mulkin kasar don bashi kafar takara karo na uku.

Shugaba Mouhamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar ya ce ba zai yi wani gyara ga kudin tsarin mulkin kasar ba ta yadda zai ba shi damar tsayawa takara kar na uku a zaben kasar. Shugaba Issoufou ya ce burin shi bai wuce na ya tsara zabe mai tsafta ba a kasar, ta yadda zai mika mulki ga wanda ya lashe zaben 2021.

Mouhammadou Issoufou ya fadi hakan ne a hirar da ya yi da tasahr talabijin na kasar, shekara guda da zabensa karo na biyu. Dan shekaru 65 a duniya, Shugaba Issoufou ya sake zama shugaban Nijar na wasu shekaru 5 ne a zaben watan Maris na bara, zaben da ‘yan adawar kasar suka kaurace masa.