MORGAN TSVANGIRAI YA KAWO ZIYARA A NAN JAMUS. | Siyasa | DW | 25.11.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MORGAN TSVANGIRAI YA KAWO ZIYARA A NAN JAMUS.

A wata ziyarar da shugaban adawar kasar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai ya kawo a nan Jamus, ya yi fira da `yan jaridu a wani taron maneman labarai da ya kira a birnin Berlin, a kan halin da ake ciki yanzu a kasarsa.

Shugaban adawar kasar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai.

Shugaban adawar kasar Zimbabwe, Morgan Tsvangirai.

Shugaban adawwar kasar Zimbawe, Morgan Tsvangirai, wanda a halin yanzu ke shawarwari da jami’an gwamnatin Jamus, a ziyarar da ya kawo a birnin Berlin, ya kira wani taron maneman labarai a babban birnin na tarayya, inda ya yi Allah wadai da dokokin kama karya da gwamnatin shugaba Mugabe ke zartarwa don, kamar yadda ya bayyanar, ci gaba da take hakkin dan Adam a kasar. Bisa cewar Tsvangirai dai:-

"Akwai kundin dokoki daban-daban, wadanda a kwanakin bayan nan ake ta zartad da su, alal misali kamar dokar nan ta kungiyoyin sa kai, ko kuma NGO. Wannan dokar, burinta ne haramta wa kungiyoyin sa kan karbar taimakon kudade daga ketare, musamman ma dai kungiyoyin da ke fafutukar kare hakkin dan Adam."

Ire-iren wadannan dokokin da Tsvangirai ke ambatarsu dai, akwai su tuli a kasar ta Zimbabwe. Ko yaushe shugaba Mugabe ya sanya hannu a kan ko wannensu, za su fara aiki kai tsaye. A halin da ake ciki yanzu dai, duk wata kungiya a kasar, ko da ta tallafa wa marasa galihu da abinci da magunguna ne, to dole ne ta yi rajista da kafofin gwamnati, in ko ba haka ba, za a haramta ta. Bugu da kari kuma, bisa sabbin ka’idojin da Majalisar kasar ta zartar, an haramta wa duk kungiyoyin kasashen ketare tsoma baki a harkokin da suka shafi hakkin dan Adam a kasar. Wasu kafofin yada labarai sun ari bakin shugaba Mugabe yana mai cewar, kafa wannan dokar ta zamo tilas ne, saboda yunkurin da wasu banagrorin ketare ke yi na tsoma baki a harkokin cikin gida na kasar, da kuma turo `yan leken asiri don su ta da rudami a lokacin zaben kasar a cikin watan Maris mai zuwa, da burin hambarad da gwamnatin kasar ta yanzu.

Morgan Tsvangirai dai, ya yi kakkausar suka ga zartad da dokar da Majalisar kasar ta yi. Yin hakan, inji shugaban adawar, wani mataki ne na matsa wa `yan kasar lamba, da kuma hana su `yancin fadar albarkacin bakinsu, `yancin da suke da shi karkbashin tafarkin dimukradiyya. Game da halin da `yan adawan ke ciki a kasar dai, Tsvangirai ya bayyana cewa:-

"A fagen siyasa, ba a la’akari da ra’ayoyin jam’iyyun adawa. Babu mai damar bayyana wani ra’ayin da ya sha bamban da na gwamnati. A ko wace rana, al’umman kasar, masu ra’ayoyi daban, na huskantar addaba ne karkashin wannan mulkin na kama karya. Akwai dimbin yawan kararraki na take hakkin dan Adam, saboda kasar yanzu ta zamo wata kafa ce ta danniya."

`Yan dawan kasar dai na ganin cewa, wannan sabuwar dokar da aka zartar, ita ce kololuwar take hakkin dan Adam a Zimbabwen. Saboda mafi yawan kungiyoyin sa kai na kasar, sun dogara ne kacokan kan samun taimako daga ketare. A halin matsin tattalin arzikin da kasar ke huskanta yanzu dai, kungiyoyin ba za su iya fatar samun ko kwabo daga gwamnatin ba. Morgan Tsvangirai ya bayyana halin tattalin arzikin da kasarsa ke ciki a yanzu ne kamar haka:-

"Da farko dai, kamata ya yi a san cewa, babu wata kasa a duniya, wadda ke huskantar komadar tattalin arziki irin ta Zimbabwe. A cikin shekaru 5 da suka wuce, mun sami komada ta kashi 50 cikin dari. Yaduwar talauci sai habbaka take yi. A wasu wuraren kasar ma, mutane ba sa samun abin da za su ci. Duk wata fatar samun kyakyawar makoma a kasar ta dusashe."

Tun da aka soke karar da aka daukaka game da shi gaban kotu a cikin watan Oktoba ne, Tsvangirai ya fara kai ziyara a kasashen ketare. Da farko dai, ya kai ziyara ne a Afirka Ta Kudu. Amma nan bai sami wani gagarumin goyon baya ba, saboda har ila yau shugaba Thabo Mbeki na Afirka Ta Kudun, yana kiyaye huldar da ke tsakaninsa ne da shugaba Mugabe. A jiya laraba ma, sai da aka yi muhawara kan sanya wa Zimbabwen da Sudan takunkumin tattalin arziki a Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniya. Amma ba a cim ma zartad da kuduri ba, saboda babakeren da Afirka Ta Kudu ta yi.

Yanzu dai fatar Morgan Tsvangirai ita ce, a wannan bulaguron da yake yi a kasashen Turai , ya sami cikakken goyon baya a kan sukar da yake yi wa matakan take hakkin dan Adam a kasarsa.

 • Kwanan wata 25.11.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BveQ
 • Kwanan wata 25.11.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BveQ