1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Montenegro zata yi shailar samun ´yanci daga Sabiya

June 3, 2006
https://p.dw.com/p/BuvU
Montenegro ta fara shirye shiryen yin shailar samun ´yancinta daga tarayyar Sabiya. Yanzu haka dai majalisar dokoki na wani zama na musamman a birnin Podgorica akan wannan batu. Ana sa rai wakilan majalisar zasu amince da daftarin shailar da Montenegro zata yi na zama kasa mai cikakken ´yanci. Wasu ´yan adawa dake goyon bayan ci-gaba da kasaancewa cikin tarayya da Sabiya sun kauracewa zaman majalisar. Kimanin kashi 55 cikin 100 na masu zabe suka kada kuri´ar amincewa da ballewa daga Sabiya a kuri´ar raba gardama da aka gudanar a Montenegro kusan makonni biyu da suka wuce.