1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moktada Sadr ya bayyana janyewar ministocin ƙungiyar sa ta Schi´a daga gwamnatin Irak

April 16, 2007
https://p.dw.com/p/BuNc

Shugaban Ɗarikar Schi´a na ƙasar Irak Moktad Assadar,ya ce yau ne ministocin ƙungiyar su guda 6 za su fita daga gwamnati.

Sadar ya ɗauki wannan mataki, domin nuna adawa da manufar Praminista Nuri Al Maliki na ƙin bayyana tsarin fitar sojnoji Amurika daga kasar Iraki.

Moktad Assadar, na daga masu nuna mummunar adawa ga zaman sojojin Amurika a ƙasar Irak, a game da haka ne ma ranar 9 ga watan da mu ek ciki ƙungiyar sata shirya wata ƙasaittatar zanga-zanga albarakacin cikwan shekaru 3 da kiffar da gwamnatin mirganyi Saddam Hussain.

A ci gaba kuma da tashe-tashen hankulla a kasar ta Irak,yan kunar baƙin wake, sun kai hare sabin hare-hare ga sojojin Amurika, inda a nan take, 3 su ka rasa rayuka a yammancin jiya.

Daga farko wannan wata zuwa yanzu su ne cikamakon sojoji 42, da Amurika ta rasa a Irak.

Sannan baki ɗaya, daga farkon yaƙin a watan Maris na shekara ta 2003, zuwa yau,Amurika ta yi assara sojoji kussan dubu 3 da ɗari 3 a Iraki.