Mohamed El Baradei ya kai ziyara aiki a ƙasar Iran | Labarai | DW | 13.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mohamed El Baradei ya kai ziyara aiki a ƙasar Iran

Shugaban hukumar Majalisar Ɗinki Dunia mai yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea Mohamed El Bararadei ya kai ziyara aiki a ƙasar Iran.

Jim kaɗan bayan saukar sa a birninTeheran ya bayyana wa manema labarai dalilin wannan ziyara.

Ya ce, ya zo ne da nufin sake gayyatar hukumomin Iran, da su watsi da matakin da su ka ɗauka.

Wannan ziyara, ta biwo bayan kalamomin shugaban ƙasar Iran, Mahamud Ahmadinedjad, inda ya bayana cewar, babu gudu babu ja da baya, a game da aniyar Iran ta sarrafa Uranium, da nufin samar da makamashin nuklea.

A yanzu haka, ƙasasen turai da Amurika, na ci gaba da Allah wadai, da wannan kalamomi.

Komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya ba ƙasar Iran wa´adin 28 ga watan da mu ke ciki, domin watsi da wannan mataki.

Sannan, Mohamed El Baradei, ya gabatar da rahoton ranar 29 ga watan Aprul, wanda zai bayyana inda aka kwana.

A jawabin da ta yi jiya, sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, ta ce hanya ɗaya tilo, da ta rage yanzu, itace ɗaukar matakai tsatsaura, na ladabtar da ƙasar Iran.

Ranar 18 ga wannan wata,za a zaman taro na musamman a Rasha,tsakanin kasashe masu kujerun dindindin a Komitin sulhu, da Kuma Jamus, a game da rikicin na Iran.