Mo Ibrahim da taimakon Afurka | Zamantakewa | DW | 12.03.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Mo Ibrahim da taimakon Afurka

Sanannen Dan Kasuwar Sudan ya lashi takobin inganta demokradiyya a Afurka

default

Demokradiyya a Afurka

Hamshakin dan kasuwar nan na kasar Sudan da ake kira Mo Ibrahim ya lashi takobin tabbatar da ci gaban mulkin demokradiyya da halin sanin ya kamata tsakanin jami'an siyasa a nahiyar Afurka. To ko wane ne wannan dan kasuwa, wanda ya ware wasu miliyoyin dala a matsayin lada ga duk wani shugaban da ake yaba masa da mulki na gari a nahiyar Afurka.

A cikin kididdigar cibiyar Forbes dangane da hamshakan mawadata a duniya Mo Ibrahim na a matsayi na 462, wato a wajejen tsakiyar hamshakan masu kudin da cibiyar ta rattaba sunayensu. Amma idan an yi batu a game da raya makomar nahiyar Afurka Mo Ibrahim shi ne akan gaba wajen ba da gudummawar kudi. Hamshakin dan kasuwar, haifaffen kasar Sudan, wanda kuma a halin yanzu haka yake da zama a Birtaniya, shi ne mallakar kamfanin salulan nan na Celtel, wanda ke gudanar da ayyukan sadarwa ta wayar tafi da gidanka a kasashe 15 na Afurka, kuma babban abin da ya sa gaba shi ne ganin kungiyoyin farar hula sun samu kakkarfan matsayi a wannan nahiya. Ya ce a Afurka ne Allah Yayi masa arziki kuma a saboda haka yake fatan al'umar nahiyar su ci gajiyar wannan arziki. Baya kaunar ganin kasashen Afurka sun ci gaba da dogara akan taimakon raya kasa, musamman ma ta la'akari da dimbin arzikin da Allah Ya fuwace musu. Mo Ibrahim yayi bayani yana mai cewar:

"Na yi imanin cewar Allah Ya albarkaci nahiyarmu da dimbin arziki. Muna da albarkatun kasa da matasa masu jini a jika. A saboda haka bana zaton muna bukatar wani taimako daga ketare. Buri na shi ne ranar da za'a wayi gari Afurka ta zama ita ce mai bayarwa, amma ba mai karba ba."

Bisa ga ra'ayin Mo Ibrahim kafar cin gajiyar wannan arzikin ga al'umar kasa ya danganta ne da salon tafiyar da mulki a kasashen da lamarin ya shafa a wawware. Akwai dai misalai da yawa a game da wannan batu, inda a kasashe kamar Nijeriya ko Angola mutane ke dada shiga mawuyacin hali na talauci duk da dimbin arzikin da Allah Ya fuwace musu. Wannan shi ne ainifin abin da ya iza keyar Mo Ibrahim ya tsayar da shawarar gabatar da zunzurutun kudi na dalar Amurka miliyan biyar, wuri-na-gugan wuri ga duk shugaban da aka yaba masa da mulki na gari a Afurka, wanda a shekara da ta wuce aka mika wa shugaba Chissano na Muzambik. An yaba wa shugaba akan irin rawar da ya taka wajen tsame kasarsa daga mawuyacin halin da ya biyo-bayan yakin basasarta yana mai gabatar da nagartattun manufofi na raya makomarta kuma bai makale kamar kaska akan kujerar mulki ba. Mo Ibrahim ya ce irin wadannan shugabannin ake bukata a Afurka, amma ba wadanda ke ikirarin cewar tsarin mulkin demokradiyya shigen na kasashen yammaci bai dace da Afurka ba. Ya kuma kara da cewar:

"Walwala da girmama 'yancin dan-Adam hakki ne na kowa-da-kowa, babu wani banbanci tsakanin kasashen Turai da na Afurka. A saboda shi ikirarin banbance-bancen al'adu da salon tunani da ake yi duk zancen banza ne. Idan ma mun lura su kansu shuagabannin dake wannan ikirarin suke amfani da motoci na alfarma kirar Jamus ko na'ura mai kwakwalwa da dai sauran kayayyin alatu daga kasashen Turai. Amma a daya bangaren basa kaunar da a shigo da mulkin demokradiyya ko wata manufa ta girmama hakkin dan-Adam daga ketare."

Shi dai hamshakin dan kasuwar daga kasar Sudan baya kaunar yin shisshigi ko tsoma bakinsa a manufofi na siyasa saboda wannan alhaki ne da ya rataya wuyan al'umar kasashen da lamarin ya shafa a wawware.