1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miyagun ayyuka na Yaki a Rwanda

Ibrahim SaniNovember 16, 2007
https://p.dw.com/p/CI71

Ƙotun ƙasa da ƙasa dake sauraren miyagun laifuffuka na yaƙi a Rwanda, ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 11 ga tsohon magajin garin Bicumbi. Ƙotun ta ce ta samu Mr Juvenal Rugambarara da laifin hannu a kisan kiyashi daya faru a ƙasarne, a shekara ta 1994.Mr Juvenal ɗan ƙabilar Hutu dake da shekaru 48, tuni ya amsa wannan laifi da ake tuhumarsa da aikatawa. Ƙotun dake zamanta a birnin Arusha na ƙasar Tanzaniya, na tuhumar waɗanda ake zargine da hannu, a kisan kiyashin da akayiwa ´Yan Ƙabilar Tutsi ne. An wancan lokaci, rahotanni sun shaidar da cewa ´Yan Ƙabilar Tutsi kusan dubu 800 ne aka halaka.