Ministocin turai sun amince kan musayar bayanai tsakaninsu | Labarai | DW | 15.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministocin turai sun amince kan musayar bayanai tsakaninsu

Ministocin harkokin cikin gida da na sharia na kungiyar taraiyar turai sun amince da baiwa juna damar shiga dinsu a kokarinsu na dakile aiyukan taadanci da matsalar bakin haure.

Jamian kasashen kungiyar 27 sun amince wajen taronsu a birnin Dresden cewa akwai bukatar bude aiyukan bincike da musayar bayanai tsakaninsu.

Dokokin zasu kuma baiwa dukkanin kasashe membobi dama samun bayanan na dangartakar mutane dana zanen hannunsu da kuma rajistar ababen hawa.

Ana sa ran taron zai kuma tattauna hanyoyin karin hadin kai don hana kwarowar baki zuwa kasashen turai.