Ministocin jam’iyyar Likud ta kasar Isra’ila sun ki bin umarnin shugabansu na yin murabus. | Labarai | DW | 12.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministocin jam’iyyar Likud ta kasar Isra’ila sun ki bin umarnin shugabansu na yin murabus.

Ministoci hudu na jam’iyyar Likud ta kasar Isra’ila, sun ki bin kiran da sabon shugaban jam’iyyar Benjamin Netanyahu ya yi musu na su yi murabus daga gwamnatin Firamiya Ariel Sharon. A jiya ne dai shi Netanyahun ya bukaci ministan harkokin waje Sylvan Shalom, da Limor Livnat, ministan ilimi, da Israel Katz, ministan noma da kuma Danny Naveh, ministan kiwon lafiya da su mika takardar murabus dinsu daga gwamnatin, kafin jam’iyyar ta Likud ta zabi `yan takaranta a zaben kasar da za a gudanar a ran 28 ga watan Maris mai zuwa.

Gidan rediyon Isra’ila ya ce ministocin dai na ganin watta makarkashiya Netanyahun ke son shirya musu kafin zaben jami’an da su tsaya takara karkashin tutar jam’iyyar Likud din.