Ministocin harkokin cikin gida na ƙasashe 6 na EU na taro a Birtaniya don tattauna batun ƙaura. | Labarai | DW | 26.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministocin harkokin cikin gida na ƙasashe 6 na EU na taro a Birtaniya don tattauna batun ƙaura.

Ministocin harkokin cikin gida na ƙasashe 6 mafi girma a Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, sun fara wani taro a garin Stratford-upon-Avon, a Ingila don tattauna batun miyagun laifuffuka da gungun ’yan daba ke aikatawa da kuma tsara manufofin bai ɗaya wajen tinkarar matsalar ƙaura zuwa ƙasashensu daga ƙetare. Rahotanni sun ce ministan harkokin cikin gidan Jamus, Wolfgang Schäuble da takwaran aikinsa na Faransa, Nicolas Sarkozy na cikin masu ba da ƙaimi wajen ganin cewa an ƙiƙiro manufofin bai ɗaya a kan wannan batun. Manufofin dai za su tanadi kafa wata hukuma ne ta Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, wadda ita ce za ta dinga kula da batun maneman mafaka. Kazalika kuma za a ƙikiro wani salo na buɗe kasauwar ƙwadagon ƙungiyar ga ma’aikata daga ƙetare har tsawon wani lokaci na wucin gadi. Ministocin sauran ƙasashen da suka halarci taron sun haɗa ne, ban da Birtaniya mai karbar baƙwancin, da Spain, da Italiya da kuma Poland. Sauran batutuwan da ke kan ajandar taron sun haɗa ne da yadda ƙasashen za su tinkari haɓakar yawan masu bin tsatsaurar ra’ayi a cikin matasa musulmi na nahiyar Turai da kuma irin goyon bayan da za su bai wa masu sassaucin ra’ayi.