Ministocin hamas sun fara aiki | Labarai | DW | 30.03.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministocin hamas sun fara aiki

A yaune ministocin gwamnatin Hamas suka fara shiga ofishisoshinsu domin gudanar harkoki na mulki,ayayinda kasashen turai ke cigaba da barazanar dakatar da tallafawa gwamnatin Palasdinun idan har bata shiga taitayinta ba.Hamas,kungiyar data samu rinjaye a zaben yankin daya gudana a ranar 25 ga watan Janairu dai,taki watsi da tsattsauran raayinta ,kamar yadda kasashen turai suka bukaci tayi,na laakari da Izraela a matsayin yantacciyar kasa,da kuma amincewa dukkan yarjeniyoyi da aka cimma tsakanin bangarorin biyu a baya.Amurka da kungiyar gamayyar turai dai sun lissafta Hamas da kasancewa daya daga cikin kungiyoyin yan taadda.QA jiya nedai shugaba Mahmoud Abbas na yankin Palasdinawa ,ya rantsar da sabbin ministocin gwamnatin hamas din gudada 24,a gabar yamma da kogin jordan da kuma zirin gaza.Mafi yawa daga cikin ministocin dai basu da ikon tafiya tsakanin yankunan biyu,saboda takunkumin tafiye tafiye da Izraela ta kakabawa yan kungiyar ta Hamas.

 • Kwanan wata 30.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu79
 • Kwanan wata 30.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu79