Ministoci uku na jam´iyar Likud sun fice daga gwamnatin Isra´ila | Labarai | DW | 13.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministoci uku na jam´iyar Likud sun fice daga gwamnatin Isra´ila

Ministoci 3 na jam´iyar Likud sun fice daga majalisar ministocin gwamnatin gamin gambizar FM rikon kwaryar Isra´ila Ehud Olmert. Nan ba da dadewa bane kuma ake sa ran yin murabus din mutum na 4 kuma ministan harkokin wajen Isra´ila Silvan Shalom. Tun a cikin makon jiya shugaban jam´iyar Likud Benjamin Netanyahu ya ba da sanarwar murabus din ´ya´yan jam´iyar su 4 daga cikin gwamnati, to amma aka dage yin haka saboda rashin lafiyar da FM Ariel Sharon ke fama da shi. Masharhanta sun ce nan da kwanaki kadan masu zuwa mista Olmert zai nada sabbin ministoci daga sabuwar jam´iyar da Sharon ya kafa wato Kadima.