Ministoci 18 sun yi murabus daga gwamnatin riƙwan ƙwaryar Somalia | Labarai | DW | 27.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministoci 18 sun yi murabus daga gwamnatin riƙwan ƙwaryar Somalia

Ministoci 18 sun yi murabus, daga gwamnatin riƙwan ƙwarya a Somalia.

Ministocin sun ɗauki matakin, don nuna adawa ga tafiyar da mulkin praminista Ali Mohamed Gedi, mussamman bayan izinin da ya ba ƙasar Ethiopia, na jibge dakaru a Baidoa.

A makon da ya gabata ne, hukumomin Addis Ababa, su ka yanke shawara tura tawagar sojoji a Somalia, domin kariya ga gwamnatin riƙwan ƙwarya, wace ke fuskantar barazanar juyin mulki, daga dakarun kotunan musulunci, wanda a halin yanlin yanzu, ke riƙe da yankuna da dama da ƙasar da su ka haɗa da Mogadiscio.

Murabis din ya wakana jim kaɗan kamin Majalisar dokokin ta kada kuri´a a game da zaman dakarun Ethiopia a Somalia da sallon tafiyar da mulkin Praminista wanda,

ya ƙagauta da kai hari ga birnin Mogadiscio domin ƙwato sa, daga hannun kotunan musulunci, tare da taimakon dakarun Ethiopia.

Ministocin da su ka yi murabus sun nunar da ƙin amincewa da anfani da ƙarfin soja wajennwartware rikicin Somalia da ta share shekaru 14, cikin yaƙen -yaƙen bassassa.