1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministan tsaron Jamus na kan hanyarsa zua Kwango.

Minstan tsaron Jamus, Franz-Josef Jung, ya tashi yau daga birnin Berlin don kai ziyara a ƙasashen Jumhuriyar Dimukraɗiyya ta Kwango da kuma Gabon. Wannan ziyarar dai na dangane ne da girke dakarun Jamus da za a yi a ƙasashen biyu, ƙarƙashin laimar rundunar kare zaman lafiyar da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai za ta tura a Kwangon, don tabbatad da tsaro a loakcin zaɓen ƙasar, wanda za a gudanar a ƙarshen wannan watan.

Ministan ya faɗa wa maneman labarai cewa, sojojin za su dawo gida kafin kirismeti. A ziyara tasa dai, Franz-Josef Jung, zai yi rangadin wasu sansanonin soji ne a biranen Kinshasa da kuma Libreville, sa’annan kuma ya tattauna batutuwan da suka shafi harkokin siyasa da shugabannin yankin. A nan Jamus dai, an yi ta muhawara mai tsanani kan girke dakarun a Kwango, saboda ganin hakan da ake yi tamkar wata babbar kasada, duk kuma da amincewa da shirin, da Majalisar dokoki ta Bundestag ta yi.