Ministan tsaron Isra´ila Mofaz ya canza sheka zuwa jam´iyar Kadima | Labarai | DW | 11.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministan tsaron Isra´ila Mofaz ya canza sheka zuwa jam´iyar Kadima

Ministan tsaron Isra´ila Shaul Mofaz ya zama babban dan siyasar kasar na 7 da ya canza sheka daga jam´iyar Likud zuwa sabuwar jam´iyar Kadima ta FM Ariel Sharon. Mista Mofaz ya ce dalilin daukar wannan mataki na sa shi ne a halin yanzu masu matsanancin ra´ayi sun yiwa jam´iyar ta Likud kakagida. Mofaz ya fadawa wani taron manema labarai cewa abin bakin ciki ne ganin yadda yanzu jam´iyar ta Likud ta fuskanci wata alkibla ta masu tsattsauran ra´ayin siyasa. Yanzu haka dai in banda tsohon FM Benjamin Netanyahu da ministan harkokin waje Silvan Shalom dukkan manyan ´yan siyasar kasar sun fice daga jam´iyar ta Likud.