1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministan tsaro Jamus ya yi kira a rage yawan sojojin kasar a ketare

Ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung ya bawa majalisar ministocin Jamus shawarar rage yawan dakarun kasar da ke aikin yaki da ta´addanci a ketare. Jaridar Welt am Sontag ta rawaito ministan na cewa kamata yayi a rage yawan dakarun da sojoji 400 wato izuwa dubu 1 da 400. Ta haka ministan wanda dan jam´iyar CDU ne zai saukaka shawo kan jam´iyar SPD don ta amince da wani sabon tsari na aikin rundunar wadda ake kai ruwa rana kanta. Wannan tsari ya tanadi tura sojojin kundunbala 100 zuwa Afghanistan tare da ba da jiragen ruwan yakin kasar ga aikin yaki da ta´addanci a yankin Kahon Afirka da kuma gabashin Tekun Bahar Rum.