1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Niebel Mosambik

January 13, 2010

Ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel ya kammala ziyararsa ta farko ga ƙasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/LUfx
Ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk NiebelHoto: AP

Bisa ga dukkan alamu an samu canjin ra'ayi dangane da shawarar da ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa ya ɗauka da farko game da ɗariɗari da taimakon kuɗi don cike giɓin kasafin kuɗin wasu ƙasashe na Afirka, bayan ziyarar da ministan ya kai ga kasashen Ruwanda da Muzambik dake samu cikakken taimakon kuɗi daga Jamus. Domin kuwa wannan taimakon shi ne babban sharaɗin musayar yawu tsakanin sassan biyu a game da demoƙraɗiyya da shugabanci na gari.

Bundesentwicklungsminister Niebel in Ruanda Afrika
Dirk Niebel a RuwandaHoto: picture-alliance/ dpa

Irin waɗannan shawarwari tsakanin ƙasashe masu ba da taimako da wɗanda ke samun taimakon zai iya kasancewa mai matuƙar amfani tare da tantance sharuɗɗan ma'amallar raya ƙasa. A cikin alfahari ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel ya faɗa wa manema labarai dake masa rakiya a ziyarar tasa ga ƙasashen Afirka cewar a sakamakon tsattsauran gargaɗi daga ɓangaren Jamus gwamnatin Uganda ta janye daga shawarar da ta ɗauka game da tsaurara dokokin hukunta 'yan luwaɗi.

"Ina matuƙar murna game da cewar ministan kula da matakan zuba jari na ƙasar Uganda ya fito fili ya bayyana cewar kamata yayi a sake tunani game da shawarar tsaurara dokar hukunta 'yan luwaɗi na zartar musu da hukuncin kisa. Idan har wannan maganar ta kai ga fadar shugaba da majalisar dokoki hakan zai zama wata nasara ta diplomasiyya a fakaice."

Sai dai fa ba maganar manufofin diplomasiyya a fakaice ne kawai ake buƙata ba, kazalika wajibi ne a zayyana wasu tabbatattun sharuɗɗa. Ƙasashe masu ba wa Uganda taimakon kuɗi don cike giɓin kasafin kuɗinta sun yi wa Uganda barazana. A can Muzambik ma ƙasashe masu ba da taimakon ba su gamsu da halin siyasa da ƙasar ke ciki ba. Ana fama da mummunan cin hanci da karɓar rashawa da kuma rashin wani nagartaccen shugabanci a ƙasar. An fuskanci maguɗi a zaɓen ƙasar da aka gudanar watan oktoban da ya wuce. Hakan ya kai ga ƙasashe 19 dake ba da taimako da su gabatar mata da abin da suka kira tattaunawa ta basira da neman wata ƙwaƙƙwarar sanarwa daga gwamnati. Amma bayan ziyararsa ga Ruwanda da ita kanta Muzambik, ministan taimakon raya ƙasashe masu tasowa na Jamus Dirk Niebel ya ankara da muhimmancin ba da taimakon kasafin kuɗin, wanda ya kama kashi 50% na kasafin kuɗin ƙasashen biyu. An dai saurara daga bakin ministan harkokin wajen Muzambik Oldemiro Baloi yana mai nuna rashin gamsuwarsa da matsin lambar ƙasashe masu ba da taimakon inda yake cewar:

Bundesentwicklungsminister Niebel in Mosambik Afrika
Dirk Niebel a MuzambikHoto: picture-alliance/ dpa

"Shawarwari tsakaninmu da ƙasashen ji ita na tafiya ne akan wata sibga ta musayar ra'ayi akan batutuwa da dama. Ba lamari ne mai sauƙi ba game da tattaunawa da ƘTT da ta G19. Kuma bayan zaɓen da aka gudanar an fiskanci tsaurin dangantaka. Abin da ya ci mana tuwo a ƙwarya shi ne take-takensu. Shi ya cancanta a yi amfani da taimakon don matsin lamba. Amma a yanzu ga alamu al'amura sun fara sararawa a dangantakarmu da juna."

A nasa ɓangaren minista Niebel dai ya nuna gamsuwarsa da irin ci gaban da ya lura da shi a Muzabik inda ya ce ƙasar na kan wata hanya madaidaiciya ta samun ci gaba bisa manufa.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu