Ministan raya ƙasashe masu tasowa na Jamus na shan suka game da sauyin manufa | Siyasa | DW | 17.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ministan raya ƙasashe masu tasowa na Jamus na shan suka game da sauyin manufa

Masu nazarin alamuran yau da kullum na yin suka game da ƙokarin da ake na canja alƙiblar manufar raya ƙasashe masu tasowa a Jamus

default

Dirk Niebel, Ministan raya ƙasashe masu tasowa na Jamus

Tun daga watan Oktoban bara ne dai aka naɗa ɗan jam'iyyar FDP, Dirk Niebel, a matsayin ministan haɗin-gwiwa da raya ƙasashe masu tasowa. To sai dai kuma tuni masu nazari akan al'amuran yau da kullum suka fara yi masa suka game da yi wa tsarin tattalin arzikin jamus babakere. A ma cikin yaƙinsa na neman zaɓe sai da Niebel ya nuna gurinsa na samun wannan muƙami . Amma kuma sai gashi yanzu yana amfani da muƙaminsa wajen samun kusanta da manufar tattakli arziƙi, a maimakon mai da hanakali ga manufar raya ƙasashe masu tasowa.

A lokacin da yake shirin yin rangadin wasu ƙasashen Asiya da suka haɗa da Vietnam da Kambodiya, Dirk Neibel, ya ce a yayin ziyarar tasa zai miƙa buƙatar samun masu saka jari a kamfanonin Jamus daga ƙasashen biyu. Kuma a matsayin abin da ya kira aikin da ya zamo wajibi akansa, zai nemi kyakyawan yanayi na yin haɗin-gwiwar tattalin arziƙi da ƙasashe da ke samun ci gaba a cikin gaggawa, irinsu Indonesia da Indiya. Sai dai kuma masu ruwa da tsaƙi a aikin raya ƙasashe masu tasowa sun yi suka game da wannan manufa da cewa manufa ce da ta saɓa wa aikin raya ƙasashe masu tasowa wadda kuma za ta nemi biyan buƙatun tattalin arzikin Jamus a maimakon cimma manufar raya ƙasashe. Ulrich Post, shugaban rukunin VERNO wanda rukuni ne na haɗin-gwiwar ƙungiyoyin masu zaman kansu guda 120 a nan Jamus ya bayyana shakku game da haka yana mai cewa:

"Ba ni da masaniya game da wani kamfanin Jamus da ke Burkina Faso ko Myammar ko kuma wata ƙasa daban da ke fama da talauci da za a iya saka jari a cikinta har Jamus ta iya cin gajiyar saka jarin. Kuma na yi imani cewa a wasu lokuta ministan zai buƙaci nuna sassauci game da haka."

A Jamus dai aikin haɗin-gwiwar tattalin arziƙi da sauran sassa da suka haɗa ba da na taimakon jinƙai fagage ne da ke ƙarƙashin manufar raya ƙasashe masu tasowa. Amma yanzu masu nazari akan al'amuran yau da kullum na bayyana fargabar cewa za a durkusar da matsayin aikin haɗin-gwiwa zuwa matsayi na aikin tattalin arziƙi da ba zai iya yin wani tasiri na azo a gani ba. Hakan kuwa wani mataki ne da ka iya biyan buƙatun masana'antun Jamus. Uwe Kekeritz, ɗan majalisa ne na jam'iyyar "The Green". Yana mai ra'ayin cewa bai dace ba a fi mai da hankali ga samun ci gaban tattalin arziƙi a maimakon cimma manufar raya ƙasashe masu tasowa. Akan haka ya ƙara da cewa:"Ba wai ina adawa ne da manufar sama wa Jamus riba daga akin haɗin-gwiwa ba. Amma wajibi ne a ba da fifiko ga buƙatun ƙasashe masu tasowa, amma ba buƙatun manyan kamfanoni ba."

Dirk Niebel, ya fito fili yana mai bayyana buƙatar samun ƙaruwar ribar da Jamus ke samu daga aikin raya ƙasashe masu tasowa da kashi ɗigo bakwai daga cikin ɗari nan da shekara ta 2015. Ya faɗi haka ne yana mai kafa hujja da cewa, kamata yayi amfanin da za a samu ya dace da aikin da aka yi. Karin Roth, mamba ce ta jam'iyyar SPD da ke aiki da komitin kula da manufar raya ƙasashe masu tasowa. Ta yi suka game da haka tana mai cewa:

"Wannan dai wani rikici da ya tanada da ba zai iya yin wani kataɓus ba, face janyo rashin yarda game da manufar Jamus ta raya ƙasashe masu tasowa. Al'uma dai sun samu wayewa sosai. Suna ba da gagarumar gudunmuwa ta kuɗi . Sun kuma amince da manufarmu ta raya ƙasashe masu tasowa da kuma haɗin-gwiwar tattalin arzƙi. Sabo da haka, bai dace ba a ce ana nuna wannan take-take da ke wajibta samun riba daga abin da mutun ke bayarwa . Wannan dai wani mataki, da a ƙarshe zai kawo cikas ga yardar da aka bai al'umar kasar nan."

Mawallafi: Hicham Driouich/Halimatu Abbas

Edita: Yahouza