1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministan harkokin wajen Jamus ya isa kasar Ghana

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ya isa kasar Ghana kann ziyararsa zuwa kasashen yammacin Afrika guda biyu da ya hada da Najeriya.

Tun farko a Najeriyar Steinmeier ya gana da shugaban kasa Umar Yar Aduwa a birnin Abuja.Ministan na harkokin wajen Jamus ya yabawa Najeriya saboda kokarinta ba magance rikice rikice a Afrika musamman a lardin Darfur na kasar Sudan.

Steinmeier ya sanarwa da manema labarai cewa yana maraba da shirin MDD na tura dakaru kusan 26,000 wadanda zasu game da dakarun AU

domin wanzar da zaman lafiya a Darfur.