Ministan harkokin wajen Jamus Steinmeier ya yi shakku kan Iran | Labarai | DW | 04.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministan harkokin wajen Jamus Steinmeier ya yi shakku kan Iran

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana shakkunsa a dangane da nasarar ,tattaunawar da zata gudana tsakanin jamiin kula da harkokin ketare na kungiyar gamayyar turai da babban jamiin shiga tsakani wajen warware rikicin nuclearn Iran.Adangane da ganin gazawan sakatare general na mdd Kofi Annan wajen shawo kann magatan Iran dakatar da bunkasa sinadran Uranium ne,yasa Ministan harkokin wajen na Jamus yace babu wani tudun dafawa da zaa cimma a ganawar da zai gudana tsakanin Javier Solana da Ali Larijani a wannan makon.Adangane da hakane Mr Steinmeier ya jaddada bukatar yin taka tsantsan da batun Nuclearn na Iran,idan kuwa ba haka ba hanyar komitin sulhun mdd zai kasance wajibi.

 • Kwanan wata 04.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5a
 • Kwanan wata 04.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5a