Ministan harkokin wajen Jamus Steinmeier ya yi kira da Amirka da ta yi bayani | Labarai | DW | 26.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministan harkokin wajen Jamus Steinmeier ya yi kira da Amirka da ta yi bayani

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya nuna damuwa game da zargin da aka yi cewar hukumar leken asirin Amirka CIA ta yi jigilar frsinoni cikin nahyiar Turai. Steinmeier ya ce ya na sa rai Amirka zata mayar da martani game da bukatun da sakataren harkokin wajen Birtaniya Jack Straw ya gabatar bisa manufa a madadin kungiyar tarayyar Turai. Kafofin yada labaru da da sun arwaito cewar jiragen saman dauke firsinoni da hukumar CIA ke zargi da aikata ta´adanci sun sauka a nan Jamus har sau 80 daga shekara ta 2002 zuwa 2004. A ranar litinin Steinmeier zai kai ziyarar aikinsa ta farko a Amirka.