1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan harkokin wajen Jamus Steinmeier ya isa birnin Alqahira

July 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bupg

A kuma kokarin diplomasiya na kawo karshen wannan rikici a yankin na GTT yanzu haka minsitan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya isa birnin Alqahira inda yake fara wata ziyarar yini biyu a yankin mai fama da rikici. Ministan zai gana da takwarar aikinsa na Masar Ahmed Abdul-Gheit da nufin gano bakin zaren warware wannan rikici, sannan da yamma ya karasa zuwa Isra´ila, inda a gobe lahadi zai tattauna da FM Ehud Olmert da ministar harkokin waje Zipi Livni da kuma ministan tsaro Amir Peretz. A karshe zai gana da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas. Gabanin tashinsa daga birnin Berlin mista Steinmeier ya bayyana yawan mutane musamman fararen hula da wannan rikici ya rutsa da kuma mawuyacin hali da aka shiga da cewa abin damuwa ne.