1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministan harkokin wajen Jamus akan jamusawa da akayi garkuwa da su

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier,ya baiyana a yau cewa,jamusawan nan 2 da akayi garkuwa da su a Iraki suna cikin hadari,bayan nuna hotunansu ta bidiyo da akayi,inda wadanda sukayi garkuwa da su suka bada waadin saoi 72 ga gwamnatin Jamus ta yanke hulda da gwamnatin Iraqi ko kuma su kashe su.

Steinmeier ya fadawa manema labari cewa,gwamnati tana iyaka nata kokari domin ganin an sako waddanan mutane kodayake ya sake sabunta kiransa ga wadanda suka sace jamusawan da suyiwa Allah su sako su zuwa ga iyalansu ba tare da bata lokaci ba.

Cikin sakon,mutanen sun bukaci gwamnatin Jamus data rufe ofishinta na jakadanci dake Iraki,ta dakatar da duk wata hulda da gwamnatin Iraki tare kuma da taimaka sako matan Iraqi da suka gidajen yari.

Kungiyar dai ta kira kanta Ansar al tawheed wal sunnah.