1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan harakokin wajen Zimbabwe ya ja kunnan jikadan Amurika a Harare

November 9, 2005
https://p.dw.com/p/BvLm

Ministan harakokin wajen kasar Zimbabwe ya bayana jan kunan jikadan kasar Amurika a birnin Harare, a game da shiga sharo ba shanu da ya ke ci gaba da yi, ga harakokin cikin gida na wannann kasa.

Hukumomin Zimbabwe na zargin jikadan da gabatar da wani jawabi gaban dimbin yan makaranta na Harare da Mutare, inda yayi suka da kakkausar halshe a game da cin hanci da rashawa da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Idan ba a manta ba a watan Oktober da ya wuce, jami´an tsaro a tsawan wani dan lokaci, sun dakatar da ambassada Christofer Dell, bayan sun tuhume da rasta wani sassani na fadar shugaba Robert Mugabe ba tare da izini ba.

A yammacin jiya, shugaba Robert Mugabe ya aikawa jikadan na Amurika kalamomin masu sussar rai, a game da shishigin da ya ke ga harakokin da basu shafi ba.