Ministan ƙawadago na tarayar Jamus ya ce burin manufar da gwamnati ta sanya a gaba ne, rage yawan mrasa aikin yi. | Labarai | DW | 23.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministan ƙawadago na tarayar Jamus ya ce burin manufar da gwamnati ta sanya a gaba ne, rage yawan mrasa aikin yi.

Ministan ƙwadago na tarayar Jamus, Franz Muteferring, ya ce gwamnati na ta ƙoƙarin ganin cewa an samar wa ma’aikata albashi mawadaci, wanda zai ishe su tafiyad da harkokin rayuwansu. Amma babba burin da gwamnatin ta sanya agaba shi ne rage yawan marasa aikin yi a duk faɗin tarayya. Da yake bayyana manufofin ma’aikatarsa, a taron muhawara kan kasafin kuɗin shekara mai zuwa a majalisar dokoki ta Bundestag yau a birnin Berlin, Franz Munteferring, ya ƙara da cewa:-

„Muna nufin ci gaba da gwagwarmayarmu ne, wajen ganin cewa an sami ragowar yawan marasa aikin yi a nan Jamus, jama’a da dama kuma sun sami aikin yi. Wannan dai shi ne buri na farko da ma’aikatar ƙwadago da jin daɗin jama’a ta sanya a gaba.“