1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miliyoyin mutane za su mutu a Yemen

November 20, 2017

Miliyoyin al'umar a kasar Yemen na fuskantar barazanar mutuwa sakamakon karancin abinci, sanadiyyar matakin da Saudiyya ta dauka na rufe hanyoyin kai agajin jin kai cikin gaggawa.

https://p.dw.com/p/2nw9b
Unterernährung im Jemen
Hoto: Getty Images/B. Stirton

Shugaban shirin samar da abinci na duniya Stephen Anderson, da ya bayyana hakan a wannan Litinin, ya ce barazanar ta samo asali ne daga munin yakin da Saudiyya ke jagoranta a wasu yankuna na kasar ta Yemen. Akalla dai mutum miliyon 17 daga cikin 26 a Yemen na matukar dogaro ne kan agajin kayan abinci.

Bayan tsananin sukar da kasar Saudiyyar ta sha kan toshe hanyoyin, a makon da ya gabata kasar ta yi alkawarin waiwayar matakinta na rufe filayen jirage da kuma ruwayen Yemen din, don a sami damar kai kayan agajin ga mabukata. Ko a wannan Lahadi ma sai da wani hari ta sama a lardin Jawf ya kashe fararen hula akalla 10.