Mike Huckabee ya taka rawar gani a zaben IOWA na Amirka | Labarai | DW | 04.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mike Huckabee ya taka rawar gani a zaben IOWA na Amirka

Mike Hukabee ya lashe zaben fitar da gwani da aka gudanar jiya a jahar IOWA na Amirka a ƙarkashin jam’iyar Republican. Tsohon gwamnan jahar Kansasa Huckabee ya ƙetare matakin farko a ƙoƙarinsa na shiga zaben tsayar da dan takarar shugaban Amirka da za’a yi cikin watan nuwamba na wannan shekara. A yayin da Barak Obama ya lashe zaben a karkashin jam’iyar Democrat da kashi talatin da bakwai cikin ɗari na kuri’u. Obama ya shaidawa mahallarta cewar sakamakon zaben ya nuna yadda Amirkawa suka matsu da aiwatar da canji a sha’annin siyasa. Ita kuwa Hillary Clinton ta zo matsayin na uku bayan John Edward wanda ya yi na biyu a karkashin jam’iyar Democrat..