1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mika yankin Bakassi ga ƙasar Kamaru

August 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bums

A yau ne mahukunta Nigeria ke mika yankin Bakassi mai arziki mai wanda ƙasashen biyu suka dade suna takaddama a kan sa. Bikin mika yankin wanda zai gudana a yankin Archibong dake arewacin tsibirin na Bakassi zai sami halartar jamián majalisar dinkin duniya da dana kasashen Faransa da Jamus da Amurka da Britaniya da kuma tawagar kungiyar gamaiyar Afrika tare da wakilan gwamnatocin Nigeria da Kamaru. Bayan kammala bikin ne kuma ake sa ran kasashen biyu za su gana domin tsara yadda za su shata kan iyakar gabar ruwan kasashen na su bisa hukuncin kotun kasa da kasa. Mika yankin na Bakassi zai kawo karshen takaddama mai daci da ta shiga tsakanin kasashen biyu har tsawon shekaru 13 a gamé da mallakar tsibirin.

A shekarar 1994 Kamaru ta kai Nigeria kara gaban Kotun duniya dake Hague wadda bayan tsawon shekaru ana shariá ta yanke hukuncin na mika mallakin tsibirin ga Kamaru. A farkon wannan watan ne dai Nigeria ta fara janye sojojin 3,000 daga yankin domin bin umarnin kotun ta kasa da kasa.