1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Meyer Werft, kamfanin jirgi mai tarihi

Pinado Abdu WabaSeptember 16, 2015

Kamfani na iyalin wani mutumi ne mai suna Meyer, wadanda suke kera jiragen ruwa tun 1795. Jiragen na da inganci sosai kuma sun kai euro milliyan 900.

https://p.dw.com/p/1GXNt
Meyer Werft in Papenburg DW Informationsreise
Hoto: DW/Hendra Pasuhuk

A kwana a tashi sufurin ruwa, ya zama wani babban kasuwa, inda a yanzu haka ya kai ga habakar kamfanoni masu gina jiragen ruwan daukan fasinjoji, wadanda za su iya daukar fasinjoji fiye da dubu uku a lokaci guda su kuma yi kwanaki a kan teku. A nan Jamus, akwai wani wurin sarrafa irin wadannan jiragen fasinjojin mai suna Meyer Werft, wanda ke wani karamin gari mai suna Papenburg a jihar Lower Saxony. Akwai wani kogi mai suna Ems mai tsawon kilometa 371, wanda ya ratsa cikin jihar Northrhein Westfalen, jihar da birnin Bonn ya ke zuwa Lower Saxony, da ma wasu yankunan kasar Holland, a cikin wani bangaren wannan kogi ne Kamfanin Meyer ke kera jiragen ruwan, kuma wannan sana'a ta kasance sana'ar wannan iyali tun kaka da kakanni kuma shekaru sama da 200 a yanzu zuri'a bakwai ke nan suka rike wannan sana'a.

Takaitaccen tarihin iyalin Meyer

Wani mutumi mai suna Meyer ne ya girka wannan kamfanin a shekarar 1795, kuma har yanzu wannan iyalin shi ne ke kula da sana'ar, a yanzu haka yana hanun zuri'a na shidda kuma zuri'a na bakwai na daga cikin wadanda ke jagorantar kamfanin saboda haka wannan ya tabbatar da dorewar kamfanin nan gaba. Da farko dai a cikin garin papenburg aka girka kamfanin ana sarrafa jiragen ruwa na katako, a shekarar 1872 aka fara gina na karfe. Daga shekara ta 1975 muka dawo nan inda muke sanana a shekara ta 1984 aka fara gina jiragen shakatawa a kan teku, kuma yanzu su kadai mu ke sarrafawa, a waje akwai wanda muka kammala, mai suna Norwegian Escape, sannan muna kan sarrafa Ovation of the seas, a yanzu haka dai a shirye muke mu gina jirage manya takwas ba kakkautawa daga nan har shekara ta 2020.

Tansania Dampfer Liemba auf dem Tanganjika-See
Jirgin Liemba a TanzaniyaHoto: Simon Collins

Jirgin Liemba a Tanzaniya

Akwai wani jirgi mai suna Liemba, wanda kamfanin ya gina sama da shekaru 100 da suka gabata, wanda bayan sun kammala suka yi dakon shi suka kai kasar Tanzaniya, domin a yi sufuri da shi a kan kogin Tangayika. A halin da ake ciki yanzu Liemba na cigaba da aiki a kan wannan kogi duk da cewa ta wuce yawan shekarun da dama ake so jirgi ya kwashe yana tafiya a ruwa wato 35 zuwa 45. Shekaru sama da dari biyu ba wasa ba, Mr Hackmann jami'in yada labaran kamfanin na Meyer Werft ya bayyana mana sirrin nasarar wannan iyali

"Muna yin tsari na wani tsawon lokaci ne, kuma a kowani lokaci muna kokarin sabuntawa da inganta fasahohinmu, burinmu ba samun kudi cikin gaggawa ba ne, muna so masu saye su sami biyan bukata, mu kuma mu san mun yi amfani da irin fasahar da ta dace."

Amfani da sabbin dabaru ne suka sanya Meyer Werft yin ficce

Bayan da jirgin ruwan Costa Concordia ya fadi, mutane da dama suka jikkata, kasuwar yawon bude ido a ruwan ya fiskanci koma baya, to amma da me da me ake la'akari da shi wajen yin jiragen banda naurorin da za su taimaka wajen kaucewa hatsari

"Idan mutun na maganan jiragen ruwa na fasinja, kamar jiragen sama ne, ba wai zance ne da ya tsaya tsakanin kamfanonin da masu kera jirage ba, akwai dokoki, musamman na kula da rayuka, sannan akwai dokokin tashoshi, da na yankunan da ke da iko da hanyoyin ruwan tekun da jirgin zai bi duk wadannan sai an yi la'akari da su wajen gina jirgin"

Duk mai sha'awa zai iya sayen jiragen tsakanin euro milliyan 300 zuwa 900, ya danganci yawan da ake bukata da kuma girman jirgin da ma yawan abubuwan da ake so a sa a ciki musamman fasahohi. Ma'aikata har da ma masu samun kwantiragi sun kai kusan dubu shidda a wannan kamfani, sai dai akwao korafin da ake yi dangane da muhalli, domin masunta na korafin cewa kuna hana su yin sana'arsu yadda ta dace to ko akwai matakan da kamfanin ya dauka kawo yanzu? Mr Hackmann ya yi mana karin haske

Meyer Werft in Papenburg DW Informationsreise
Norwegian Escape a kan hanyarta na barin wurin da aka keraHoto: DW/Hendra Pasuhuk

"Shekarunmu dari biyu da 20 a nan a Papenburg, saboda haka duk mutanen da ke aiki a nan saboda haka a wurinmu yankunan da ke kewaye da mu akalla kilometa 100 mu kan tabbatar mun sayi abubuwa a wurinsu, mun kuma inganta dangantakarmu da su, mu tallafawa makarantu musamman wadanda suke karatun kera jirgin ruwa, kamar dai yadda mu ke yi da kwastamomin mu haka ma muke yi da ma'aikatanmu, mu tabbatar sun sami gamsuwa."