1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mexico ta yi watsi da barazanar shugaban kasar Amirka

Zulaiha Abubakar
April 23, 2018

Ministan kasashen wajen kasar Mexico Luis Videgaray ya jaddada aniyar kasar na tafiyar da harkokin 'yan gudun hijira  ba tare da karbar umarni daga wata kasa ba.

https://p.dw.com/p/2wXK0
Mexiko | Luis Videgaray wird neuer Außenminister
Luis Videgaray ministan harkokin wajen kasar MexicoHoto: REUTERS/E. Garrido

Ya kuma kara da cewa gindaya wasu sharaddai a kan yarjejeniyar kasuwanci marar shinge na arewacin kasar Amirka zalinci ne,ministan ya yi wadannan kalamai ne bayan shugaba Donald Trump na Amirka ya yi wa kasar ta Mexico barazanar amfani da batun hana kwararar bakin haure a matsayin sharadin ci gaba da kasancewa cikin shirin yarjejeniyar kasuwanci marar shinge,in da ya kara da cewar ya zamar wa Mexico tilas ta dauki matakin hana 'yan cirani shiga kasar Amirka.