Merkel zata kai ziyarar aiki a Poland | Labarai | DW | 02.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel zata kai ziyarar aiki a Poland

A yau juma´a SGJ Angela Merkel zata kai ziyarar aiki ta farko a kasar Poland. Kakakin gwamnati a birnin Berlin ya ce Merkel ta zabi kaiwa manyan kasashen biyu makwabtan Jamus wato Faransa da kuma Poland ziyarar bayan rantsad da ita a matsayin wata alama ta nuna kyakkyawar dangantaku tsakanin kasashen. Shi kuwa a nasa bangaren FM Poland Kazimierz Marcinkiewic ya fadawa manema labarai cewa yanzu an samu wata sabuwar dama ta karfafa huldar diplomasiya tsakanin Jamus da Poland bayan sauyin gwamnatoci da aka samu a kasashen biyu. Sabuwar shugabar gwamnatin ta Jamus zata yi kokarin shawo kan hukumomi a birnin Warsaw cewa Jamus ba ta da niyar yiwa KTT babakere.