Merkel zata gana da Mubarak a Berlin | Labarai | DW | 10.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel zata gana da Mubarak a Berlin

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na shirin farfado da daftarin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya,a bangaren batutun da zata mayar da hankali bayan Jamus ta karbi akalar jagorancin KTT a shekara mai kamawa.A sakon ta na mako mako ta yanar gizo gizo zuwa ga masu zabe,Merkel ta ce yana da mughimmanci wadanda keda hannu a tattaunawar da suka hadar da Amurka da Rasha da Mdd da KTT,su dada zage dantse wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin gabas ta tsakiya dake fama da rigingimu.A shekarata 2003 nedai,tawagar ta kaddamar da abunda ta kira daftarin sulhu,dazai ja ragamar bawa Palasdinawa yantacciyaer kasa,sai dai har yanzu an gaza cimma komai.A yau nedai shugabar gamnatin Jamus Angela Merkel zata gana da shugaba Hosni Mubarak na kasar Masar A Berlin,kafin ta karbi bakuncin Prime ministan Izraela Ehud Olmert a ranar talata.