Merkel za ta tattauna da Trump | Labarai | DW | 17.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel za ta tattauna da Trump

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkle za ta gana da takwaran aikinta na Amirka Donald Trump a wata ziyara aiki da za ta fara a yau a Washington.

Ziyarar dai ta biyo bayan irin zazzafar kallaman da kasashen biyu suka rika ambatowa a tsakaninsu, tun bayan da Donal Trump ya samu nasara a zaben shugaban kasar da aka yi kusan watanni uku da suka wucce.Kasashen nahiyar Turai sun zura ido a kan wannan ganawa su ga yadda za a kwashe,to amma wani babban jami'in gwamnatin Jamus ya ce shugabar  za ta je Washington ne domin samun fahimtar juna da Donald Trump.