1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel: 'Yan gudun hijira, alheri ne a Jamus

Kamaluddeen SaniDecember 31, 2015

Angela Merkel ta yi jawabin karshen shekara inda ta yi bayani kan ribar da tarayyar Jamus za ta samu bayan 'yan gudun hjiira sun saje tare da fara gudanar da aiki. Merkel tace.

https://p.dw.com/p/1HWXa
Bundeskanzlerin Angela Merkel Neujahrsansprache
Hoto: Reuters/H. Hanschke

A cikin wani jawabin da ta gabatar ga al'ummar tarayyar Jamus shugabar gwmnatin Angela Merkel ta bayyana cewar kwararar 'yan gudun hijira zuwa kasar ka iya zama alheri ga kasar a nan gaba.

Ta ce "Ko tababa babu ci gaba da kwararar 'yan gudun hijirar na iya bukatar da tarin abubuwa daga garemu,hakan zai ci lokaci da kuzarinmu da kuma kudade musamman ta yin la'akari da namijin aikin dake gabanmu na samar wa wadanda ke bukata zama damu gurin zama."

Kazalika Angela Merkel ta yi nuni da cewar duk da sukan lamirin da wasu daga ciki da wajen kasar suke yi, kada su manta cewar dukkaninsu Jamusawa ne kuma bai kamata su nuna wa junansu kyama ba musamman ga wadanda ke neman mafaka zuwa kasar.