1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yi kira ga masu sukar Mugabe da su fuskance shi ido da ido

October 20, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8C
SGJ Angela Merkel ta kalubalancin masu sukar lamirin shugaban Zimbabwe Robert Mugabe tana mai cewa su yi magana da shi ido da ido. Merkel ta fadi haka ne a gefen taron kolin KTT a Portugal. Ta ce tana adawa da barazanar da FM Birtaniya Gordon Brown ya yi na janyewa daga taron kolin da ake shirin yi tsakanin kungiyar EU da KTA a cikin watan desamba. Merkel ta ce za´a yi sukar lamirin Mugabe kai tsaye a gaban shi idan ya halarci taron. Ta ce zata halarci taron koli ko Birtaniya ta je ko ba ta je ba. Kasar Portugal wadda ke rike da shugabancin karba karba na kungiyar EU ta ce zata aike da goron gayyata ga dukkan shugabannin Afirka ciki har da Mugabe, wanda ake zargi da tabka magudin zabe, keta hakin Bil Adama tare da jefa kasarsa cikin manyan matsaloli na tattalin arziki.