1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yi jawabin nuna alhini kan harin Munich

Salissou BoukariJuly 23, 2016

Bayan da ta fito daga zauran taron majalisar tsaron kasar Jamus, Shugabar Gwamnati Angela Merkel ta jinjina wa jami'an tsaron jihar Bavariya kan irin jan kokarinsu wajen farautar wanda ya Kai harin Munich.

https://p.dw.com/p/1JUnw
Nach Schießerei in München Angela Merkel
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gudanar da jawabi a wannan Asabar inda ta nuna damuwarta kan abubuwan da suka wakana a game da harin da wani matashin dan kasar ta Jamus mai shekaru 18 da haihuwa ya kai da yammacin ranar Jumma'a a birnin Munich. Cikin jawabin da ta gabatar, Merkel ta jinjina wa jami'an tsaron 'yan sanda na jihar Bavariya da suka nuna jan kokari da kwazo yayin wannan abin takaici da ya wakana.

Nach Schießerei in München Polizei
'Yan sandan birnin Munich na Jamus a harabar inda aka kai hariHoto: Reuters/A. Wiegmann

Ta ce: "Tunaninmu gaba daya na zuwa ne ga wadanda suka rasu yayin wannan hari, da kuma iyalansu. Wannan dare na Jumma'a wayewar Asabar, ya kasance mai wahalar gaske ga al'ummar kasar Jamus, kuma wurin da aka kai harin wuri ne da dukanninmu mukan iya samun kanmu a nan."

Daga nashi bangaren Horst Seehofer da ke a matsayin Gwamnan Jihar Bavariya inda wannan hari ya affku, ya ce suna masu cike da juyayi...

Nach Schießerei in München Horst Seehofer Kranz
Gwamnan Jihar Bavariya da sauran manyan ma'aikatan jihar yayin da suka ziyarci wurin harinHoto: picture-alliance/dpa/S. Hoppe

"Wadannan kashe-kashe da suka wakana, abu ne da ya kasance mai nauyin gaske ga dukannin al'ummar wannan Jiha ta Bavariya. kuma ina mai isar da gaisuwar ta'aziya ga iyalan wadanda suka rasu a mdain gwamnatin jihar Bavariya."

Masu bincike sun tabbatar cewa, wanda ya kai harin bashi da wata alaka da kungiyar IS, kuma daga cikin wadanda suka mutu yayin wannan hari, akwai 'yan kasar Turkiya uku, 'yan kasar Kosovo uku, dan kasar Girka daya a cewar masu binciken.