1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yi gargadi kan kyamar baki

Yusuf Bala Nayaya
January 27, 2018

Angela Merkel ta ce abu ne me kyau a yi tuni da miliyoyin mutane da suka zama cikin wadanda aka halaka don ya zama izina ga masu kin jinin baki su san abu ne mara kyau.

https://p.dw.com/p/2rczL
Screenshot Podcast Angela Merkel
Hoto: Bundeskanzlerin.de

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi gargadi na kaucewa nuna kyamar baki a kasarta, abin da ke zuwa a wannan rana da ake tuni da ranar kisan Yahudawa ta kasa da kasa da MDD ta ware a irin wannan rana inda ta ce batu ma na a ce a kare gine-ginen Yahudawa "abin kunya ne."

Ta ce abu ne me kyau a tuna da miliyoyin mutane da suka zama cikin wadanda aka halaka don ya zama izina kan kin Yahudawa da nuna kin jinin baki da nuna kyama kamar yadda Merkel ta wallafa a sakon da take fitarwa ta kafar intanet a duk mako a ranar Asabar.

Abun takaici ne da kunya a ce wuraren Yahudawa ba sa zama ba tare da basu kariya ba ko a makarantu ko wuraren ibada. Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta ce tana kan bakanta na yaki da masu kin jinin baki don haka tana kan kokari na ganin an samar da kwamishinan yaki da nuna kyamar baki a gwamnatin Jamus me zuwa muddin aka kai ga nasarar kafa gwamnatin hadaka.